Jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya EFCC, sun kama wasu mutum 105 ciki har da 'yan kasar China 4 da ake zargi da aikata zambar yanar gizo, a wani gida dake yankin Gudu a Abuja.
Sanarwar da kakakin hukumar EFCC Dele Oyewale, ya fitar a yau Juma'a, ta ce wadanda aka kama suna da alaƙa da wasu gungun 'yan damfara da ke aikata ta'asa a kasashen Turai da wasu sassan duniya.
Category
Labarai