![]() |
Jami'an hukumar EFCC |
Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci ta kama ma'aikatan revenue na Katsina bisa zargin zambar kudi ta naira biliyan 1.2 da suka shigo wa jihar daga hukumar lafiya ta duniya da sauran wasu hukumomin ketare.
Wadanda ake zargin sune: Rabiu Abdullahi, Sanusi Mohammed Yaro, Ibrahim M. Kofar Soro, Ibrahim Aliyu da Nura Lawal Kofar Sauri.
An kama su ne biyo bayan wani koke da gwamnatin jihar Katsina ta shigar na cewa wadanda ake zargin sun hada baki tare da karkatar da kudaden da suka kai N1,2 daga hannun hukumar lafiya ta duniya.
Binciken da hukumar ta yi ya nuna cewa Nura Lawal da kamfanin sa na ''NADIKKO'' da su ake amfani wajen karkatar da kudaden da aka wawure,wadannan kudade da aka wawure an gano su ne a asusun bankuna daban daban na wadanda ake zargin.
Yanzu haka dai wadanda ake zargin suna tsare a ofishin hukumar EFCC shiyyar Kano kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.