Hisbah ta ceto kananan yara mata 16 da aka yi safararsu a Kano

 


Jami’an hukumar Hisbah a jihar Kano sun yi nasarar kubutar da wasu kananan ‘yan mata su 16 da aka yi safararsu a wata tashar mota a jihar.

Wadanda lamarin ya rutsa da su, dukkansu ‘yan mata ne masu karancin shekaru, an ceto su ne a tashar mota ta Unguwa Uku.

Da yake jawabi mataimakin kwamandan Hisbah, Mujahid Aminuddeen Abubakar ya bayyana cewa jami'ansu sun yi nasarar ceto wasu mutane tare da ceto kananan yaran mata da ake shirin safarar su zuwa Legas da Jamhuriyar Benin da kuma Ghana.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp