Hauhawar farashin abinci ya ragu a 2024 da kashi biyu cikin dari idan aka kwatanta da 2023 - MDD

 

Kayan Abinci

Wani rahoto na hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyakin abinci ya ragu da kashi 2.1 cikin 100 a shekarar 2024 idan aka kwatanta da na shekarar da 2023.

Farashin kayan abincin dai yana kashi 122.0 a cikin 2024, wanda ya ragu kan kaso 2.6 cikin ɗari, a shekarar 2023.

Duk da raguwar da aka samu cikin shekara daya, hauhawar farashin kayan abinci ya tashi a watannin shekarar 2024, inda alkaluman ya nuna sun karu da kaso 117.6 daga watan Janairu zuwa 127.0 a watan Disamba, karin kashi 6.7 cikin 100 na abubuwan da suka hada da nama, mai sauran kayan abinci.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp