Haryanzu babu batun kawancen "maja" tsakanin mu da NNPP da PDP-Peter Obi

 

Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a shekarar 2023, Peter Obi, ya ce har yanzu babu batun wani kawancen "maja" da PDP, NNPP ko wata jam'iyya.


Tsohon gwamnan jihar Anambra ya bayyana haka ne a safiyar ranar Alhamis lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja kan halin da kasar ke ciki.


Ya kara da cewa har yanzu babu wata yarjejeniya tsakanin su da sauran bangarorin. Sai dai ya yi kira ga duk masoyan Nijeriya domin su taru a 2027 su kayar da APC wacce ya zarga da karkatar da dukiyar kasa.


Obi ya bayyana matsalar tsaro a kasar a matsayin abin takaici, inda ya ce ‘yan Nijeriya na mutuwa babu gaira babu dalili saboda ‘yan fashin daji, da kuma sace sacen mutane domin neman kudin fansa.


Sai dai Obi ya yi zargin cewa jami’an gwamnati sun yi almundahana da dukiyar al’umma a shekarar 2024 ta hanyar tafiye tafiye zuwa kasashen waje.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp