Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamared Shehu Sani ya ce akwai hanyoyin da za a iya wajen magance matsalar cushe da 'yan majalisa ke yi cikin kasafin kudin da hukumomi da ma’aikatun gwamnati ke gabatarwa.
Wani sakon da ya wallafa a shafin sa na sada zumunta na X, Shehu Sani yace hanya daya tilo ta magance yin cushen ita ce yin dokar da za ta haramtawa ‘yan majalisar sauya kasafin Kudin da aka gabatar musu, sai dai ya ce wannan abu ne mai wuya.
Shawarar ta Shehu Sani na zuwa ne dai dai lokacin da kwamitin kasafin kudu da ministan kudi da sauran masu ruwa da tsaki ke gudanar da wani taro a birnin tarayya Abuja.