Hakkin 'yan Nijeriya ne a samar masu da wadataccen abinci ba alfarma ba-Tajudden Abbas
Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce samar da abinci wani babban hakki ne na ‘yan kasa ba gata ba.
Abbas ya bayyana haka ne a Abuja a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a matsayin babban bako a taron tattaunawa na shekara-shekara
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya kudurin Majalisar Dokoki ta kasa na kafa dokar da za ta bunkasa noma tare da tabbatar da wadatar abinci a fadin kasar.
Shugaban majalisar ya samu wakilcin shugaban kwamitin kula da wadatar abinci na majalisar, Dike John Okafor.