![]() |
CNG |
A wani bayani da Kodinetan kungiyar na kasa Kwamared Jamilu Aliyu Charanchi ya fitar, yace wannan matakin zai ƙara jefa al'umma cikin halin matsin rayuwa da suke ciki.
Kungiyar ta nanata cewa kalaman gwamnati na tuntubar masu ruwa da tsaki shaci-faɗi ne domin 'yan Nijeriya dake shan wahalar saka kudin sadarwa ba su cikin wannan tuntubar.
Da wannan ƙarin da aka yi, kudin kira za su tashi daga N11 zuwa N16.50 duk minti ɗaya, inda tura sako zai kai N6 daga Naira 4, hakama kudin data zai tashi daga N350 zuwa N431.25 akan kowace 1gb.