Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa gwamnatin Nijeriya ta kashe naira biliyan 9 wajen gyaran layin layin lantarkin Shiroro.
Idan dai za a iya tunawa, layin wutar lantarkin ya lalace ne a watan Nuwamban shekarar 2024, lamarin da ya janyo rashin wutar lantarki na tsawon mako biyu a wasu jihohin Arewacin Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da mai baiwa ministan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bolaji Tunji ya fitar, ya ce ana ci gaba da gyara layin wutar har zuwa wannan lokaci
Ya ce TCN ta kashe naira biliyan 9 gyara tare da maido da layin wutar da wasu ‘yan ta’adda suka lalata da ya jefa wasu sassan arewacin Nijeriya cikin rashin wuta wanda har zuwa wannan lokaci ba a kammala aikin ba.