Gyaran filin wasan Abuja wanda akafi sani da Moshood Abiola Stadium zai lakume Naira biliyan 12 cikin kasafin kudin shekarar 2025

 

Filin wasan Moshood Abiola da ke Abuja a Nijeriya


Gwamnatin Nijeriya ta ware sama da Naira biliyan 12 a wannan shekara domin gyara da kuma inganta babban filin wasa na Moshood Abiola na kasa da ke Abuja.

An bayyana wannan a cikin Naira Tiriliyan 49.7 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa majalisun dokokin kasar kasafin kudin shekarar 2025,a karshen shekarar 2024.

Kamar yadda bayanin kasafin kudin ya nuna, tsohuwar ma’aikatar wasanni wadda yanzu haka take aiki a matsayin hukumar wasanni ta kasa NSC, za ta kashe Naira biliyan 12,772,951,242 wajen inganta babban filin wasan Abuja.

A cikin shekarar 2020, bayan shekaru wajen nuna rashin kulawa da filin, tsohon Ministan Wasanni, Sunday Dare, ya kaddamar da wani shiri wanda ya yi kira ga daidaikun mutane da kungiyoyi, kamfanoni da su taimaka wajen gyara filin wasan.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp