Yayin da majalisar dokokin Nijeriya ta koma aiki a yau, 'yan majalisar daga yankin arewa sun kammala shirye-shiryen rufe majalisa idan har ba a janye kudirin gyaran haraji da ke gaban majalisar ba.
Sun nanata kiran da suka yi na a janye kudirin saboda rashin tuntubar masu ruwa da tsaki game abubuwan da kudurorin suka kunsa, a cewar jaridar Dailytrust.
Don magance wadannan matsalolin, majalisar dattawa ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye Sanata Abba Moro don ganawa da babban lauyan tarayya don magance korafe-korafen da suka shafi kudirin.