Abdulrahman Abdulrazaq |
Shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya yaba wa manufofin tattalin arziki na shugaba Bola Tinubu dake kara habbaka jihohin kasar.
Abdulrazaq ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin bikin sabuwar shekara da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da mambobin kungiyar gwamnonin Nijeriya suka kai wa shugaban kasar a gidansa da ke da ke Legas.
Gwamnan ya kuma bayyana nasarorin da aka samu a harkar noma a karkashin gwamnatin Tinubu, inda ya bayar da misali da yadda aka samu amfanin noma mai yawa a jihar Jigawa.
Abdulrazaq ya baiwa shugaban tabbacin ci gaba da bayar da goyon baya wajen magance kalubalen tsaro da ci gaban tattalin arziki.