Geoge Akume |
Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya bayyana aniyar shugaba Bola Tinubu na ciyar da 'yan kasar ribar dimukradiyya ta hanyar kyautata rayuwar su.
Akume ya bayyana hakan ne a ranar Larabar a wajen taron da aka gudanar don karrama babban daraktan Kula da Gidaje ta Tarayya, Mathias Byuan, a Jihar Binuwai.
Akume, yayin da yake kaddamar da ayyukan tituna da gwamnatin tarayya ta fara aiwatarwa a fadin jihar, titin Makurdi/Mile, ya umurci matasa da su rika neman a ba su hakkinsu na tafiyar da harkokin siyasa ba kawai su zauna su yi shiru ba,su zamo masu jajircewa a koda yaushe.