Gwamnatin Tinubu na muzguna wa masu sukarta - Madugun adawa Atiku Abubakar


Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu da murkushe yan adawa.

Atiku ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani game da tsare dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC a shekarar 2023, Omoyele Sowore, da kuma tsohon babban sakataren hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS) Farfesa Usman Yusuf.

Atiku kara da cewa Tinubu da jam’iyyar APC na mayar da karfinsu wajen tsangwamar yan adawa tare da tsorata su domin su tafiyar da mulkin jam’iyya daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp