Gwamnatin tarayya ta bai wa iyalan wanda ya zana tutar Nijeriya tallafin milyan 30

 

Shugaba Tinubu

Gwamnatin tarayya ta bayar da gudummawar N30m ga iyalan wanda ya yi zanen tutar Nijeriya, Taiwo Akinkunmi, a ranar Alhamis.

Babban daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta kasa Lanre Issa Onilu tare da rakiyar daraktan hukumar na jihar Oyo Olukemi Afolayan ne suka gabatar da cakin kudin a madadin gwamnatin tarayya a fadar gwamnati da ke Elebu, Ibadan, jihar Oyo.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Marigayi Akinkunmi ya rasu ne a ranar 29 ga watan Agustan 2023, yana da shekaru 87 a duniya.

A ranar 4 ga Satumba, 2023, Shugaba Bola Tinubu ya aike da wata tawaga karkashin jagorancin ministan yada labarai da wayar da kan jama'a Mohammed Idris, domin yi wa iyalan ta'aziyya, inda gwamnatin ta yi alkawarin tallafa wa iyalan marigayin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp