Gwamnatin tarayya ta amince da fita da naira biliyan hudu domin aiwatar da shirin tallafa wa magidanta a Nijeriya da kudade.
Ministan jin kai da yaki da talauci Farfesa Nentawe Yilwada ne ya sanar da hakan a yayin kaddamar da shirin bayar da agaji na 2025 da ya gudana a Abuja.
Ministan ya ce shirin na tallafa wa magidanta miliyan 10 za a soma shi ne daga watan Fabrairu zuwa Afrilun 2025.
Category
Labarai