Gwamnatin Nijeriya za ta yi wa yara sama da miliyan 10 rejistar haihuwa cikin watanni 3


Hukumar kidayar jama'a ta Nijeriya ta ce za a yi wa yara sama da miliyan 10 rejistar haihuwa a cikin watanni uku.

Shugaban hukumar Alhaji Nasir Isa Kwara, ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan da uwar gidan shugaban kasa Sanata Oluremi Tinubu, ta gabatar da takardar haihuwa ga jariri na farko da aka haifa a sabuwar shekarar 2025.

Alhaji Nasir wanda ya samu wakilcin Kwamishinan hukumar a jihar Katsina, Bala Banya, ya ce hukumar kidaya ta dukufa don tabbatar da cewa kowane yaro an yi masa rejista a Nijeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp