Gwamnatin Nijeriya ta ware Naira biliyan 60 cikin kasafin kudin shekarar 2025 don ciyar da makarantun firamare abinci mai gina jiki a matsayin daya daga cikin sabbin tsare tsare da ma’aikatar ilimi ta kasar za ta aiwatar.
Idan dai za a iya tunawa tsohon ministan ilimi na kasar ya bayyana cewa ma’aikatar za ta gudanar da shirin ciyar da makarantu abinci mai gina jiki,kafin shugaban kasar ya tsige shi.
Sai dai an ware Naira biliyan 50 cikin kasafin kudin na shekarar 2025,domin tallafa wa shirin maido da yaran da ba sa zuwa makaranta, tare samar da kayayyakin koyo da koyarwa na zamani ga makarantun firamare da sakandare a cikin jihohi 36 da ke kasar kamar yadda Daily Trust ta rawaito.