Gwamnatin Nijeriya za ta gina gidaje dubu 10 ga ma'aikatan lafiya

 

Shugaba Tinubu

Aikin wanda ma’aikatar gidaje da raya birane ta  tare da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya ta tarayya, za tai na da nufin samar da gidaje masu sauki da inganci ga likitoci kwararru a fadin kasar.

Ministan gidaje da raya birane Ahmed Dangiwa, ya bayyana shirin samar da gidajen a wata ganawa da shugabannin kungiyar likitocin Nijeriya a ranar Alhamis, a Abuja.

Dangiwa ya jaddada mahimmancin inganta rayuwar ma’aikatan kiwon lafiya,wadanda da yawansu ke fuskantar kalubale wajen samun matsuguni, musamman a biranen da cibiyoyin kiwon lafiya suke.

Ministan ya ce yakamata ma'aikatan lafiya suna da gidajen zama da suka dace da su shiyasa ma'aikatar hadin gwiwa da ma'aikatar lafiya suka fito da wannan tsari.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp