Gwamnatin Nijeriya ta ce a shirye take domin tattaunawa da jagororin kasar Nijar domin magance rikicin da ke tsakanin kasashen biyu ta hanyar diflomasiyya.
Ministan harkokin waje na kasar Yusuf Tuggar, ne ya bayyana hakan a cikin wani bayani da ya fitar.
Ministan ya bukaci da a yi tattaunawa ta fahimtar juna tare da warware zarge-zargen da Shugaban Nijar Janar Abdourahman Tchiani ya yi wa kasar.