Gwamnatin Nijeriya ta amince da kamfanonin jirage 4 su yi jigilar maniyyata hajjin 2025


Hukumar jin dadin alhazzai ta Nijeriya ta ce gwamnatin tarayya ta amince da kamfanonin jiragen sama 4 da za su yi aikin jigilar maniyyata hajjin 2025.

Wani bayani daga shugaban hukumar NAHCON Farfesa Abdullahi Usman, ya ce kamfanoni 11 ne suka nemi wannan damar sai dai 4 kawai hukumar ta zaba.

A cewar Farfesa Abdullahi, kamfanonin da aka zaba sun haɗa da Air Peace Ltd., Fly-Nas, da Max Air, da kuma UMZA Aviation Services Ltd.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp