Gwamnatin Najeriya ta dakatar da kamfanin jiragen Max Air na wata uku bayan hatsarin da ya faru a Kano


Gwamnatin Najeriya ta dakatar da kamfanin jiragen sama na Max Air na tsawon wata uku bayan fashewar tayar jirgin a daren Talata a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, dake jihar Kano.

Da yake sanar da dakatarwar, jami'in yada labarai na hukumar lura da harkokin sufurin jirage ta Najeriya (NCAA) Micheal Achimugu, ya ce an dakatar da kamfanin na wata uku ne har sai hukumar ta NCAA ta yi kwakwaran binciken tabbatar da lafiyar jiragen kamfanin Max Air.

Lamarin na baya baya nan shi ne karo na uku cikin watanni uku da jiragen kamfanin na Max Air ke samun matsala, a cewar jaridar Dailytrust.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp