Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto ya kaddamar da rabon babura 1000 da a daidaita sahu 500 ga masu haya da aka bai wa cikin rangwame na kashi 80.
Gwamnan ya ce ya yi hakan ne domin saukaka zirga-zirga da kuma samar da ayyukan yi ga matasan jihar.
Ahmad Aliyu ya ce za a sayar da babur naira 300,000 yayin da a daidaita sahu za a sayar miliyan 1.
Category
Labarai