Gwamnatin jihar Sokoto ta gargadi mazauna jihar da su yi taka tsan tsan tare da bayar da rahoton duk wani abu na zargi ga jami'an tsaro

 

Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu

A cikin wata sanarwa da mai baiwa gwamnan jihar shawara kan al'amuran tsaro Kanar Ahmed Usman mai ritaya ya fitar, gwamnatin jihar ta bayyana irin nasarorin da sojojin hadin gwiwa ke samu, wanda ya sa ‘yan bindigar suka shiga rudani.

Sanarwar ta bayyana cewa, jami'an tsaro sun lalata yankunan ‘yan ta’adda da dama, da halaka wasunsu da tare da ceto daruruwan mutanen da aka yi garkuwa da su.

Sanarwar ta bukaci mazauna jihar da su yi taka tsan tsan tare da bayar da rahoton duk wani abun zargi a cikin al’umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp