Gwamnatin jihar Jigawa zata siyawa kakakin Majalisar jihar motar alfarma kirar Toyota Prado ta miliyan 100 tare da wata ta miliyan 100 ga mataimakin sa.
Bayanin hakan na kunshe a cikin kasafin kudin jihar na 2025 da Jaridar Solacebase ta binciko.
Haka zalika gwamnatin ta sake ware miliyan 200 na siyen motocin ga akawun majalisar da mataimakin sa.