Gwamnatin Jihar Abia ta amince karin Alawus-Alawus ga sarakunan gargajiya

 

Gwamnatin Abia ta amince da biyan wasu sarakunan gargajiya na jihar alawus alawus daga N250,000 zuwa N350,000 duk wata.

Kwamishinan yada labarai na jihar Abia, Okey Kanu ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin tattaunawa da manema labarai.

Okey Kanu ya kuma ce mambobin Majalisar Sarakunan Gargajiya a matakin jahohi da na kananan hukumomi za su rika karbar karin Naira 100,000 duk wata.

Mista Kanu ya bayyana cewa wannan mataki ne da gwamnatin jihar ta ɗauka domin ci gaban masarautun gargajiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp