Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sake nada kwamishinoni


Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin wasu mukamai na wasu muhimman mutane a gwamnatinsa ciki har da Ahmad Muhammad Speaker a matsayin mashawarci kan yada labarai.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce sauran mukaman sun hada da Injiya Ahmad a matsayin mai baiwa gwamna shawara bangaren ayyuka da Malam Sani Abdullahi Tofa bangaren ayyuka na musamman.

Gwamnan ya kuma nada Malam Sani Tofa a matsayin Khadi na kotun shari'a, kazalika da da Honarabul Ibrahim Jibrin Fagge a matsayin shugaban hukumar kula da ma'aikatan kananan hukumomi da sai Hajia Ladidi Ibrahim Garko a matsayin shugabar hukumar kula da ma'aikatan jihar Kano.

Sanarwar ta ce, gwamnan zai rantsar da wadanda aka baiwa mukaman a gobe Litinin 6 ga watan Janairun a fadar gwamnatin jihar Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp