Gwamnan jihar Ribas Similanayi Fubara ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2025 naira tiriliyan 1.188 awanni 48 bayan gabatarwa majalisar dokokin jihar

 

Gwamnan jihar Ribas Similanayi Fubara


A wannan Alhamis, 2 ga watan Janairu, 2025, Gwamnan Ribas Similanayi Fubara ya sanya hannu kan kasafin kudin 2025 tare da godewa majalisar dokokin jihar karkashin jagorancin Victor Oko-Jumbo bisa yin kyakkyawan aikin cikin awanni 48.

Gwamnan ya tabbatar da cewa majalisar dokokin wadda Oko-Jumbo ke jagoranta ita ce daya tilo da ake da ita a jihar.

Sai dai gwamna Fubara ya bayyana cewa Martins Amaewhule da wasu mambobi 26 da suka sauya sheka daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa jam’iyyar APC ba ‘yan majalisa ne ba, duk kuwa da kokarin da suka yi na janye matakin da suka dauka a kwanakin nan.

Gwamna Fubara dai ya shiga takun saka da wasu 'yan majalisun jihar da ke goyon bayan ministan Abuja Nyesom Wike, wanda daga baya suka bayyana komawar su jam'iyyar APC.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp