Gwamnan jihar Neja Mohammed Umaru Bago, ya bukaci sauran gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya dasu dauki harshen Hausa a matsayin yaren koyar da Karatu a yankin.
Bago, ya ce hakan zai taimaka sosai wajen bunkasa fannin ilimi ,kana ya bukaci shugabannin dasu sake nazarin manhajar Ilimi a Arewa.
A cewar sa daukar yaren Hausa a matsayin na koyarwa zai kara yawan yara masu shiga Makaranta tare da kara fahimtar abinda ake koyar dasu da kawo karshen matsalar yaran da basa zuwa makaranta.