A cewarsa, rabon motocin na daga cikin kudirin gwamnatin jihar na karfafa ayyukan shari’a.
Zulum, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dakta Babagana Mallumbe, ya mika makullan motocin ga babban lauyan gwamnatin jihar kuma kwamishinan shari’a, Barista Hauwa Abubakar, a ranar Jumma’a a Maiduguri babban birnin jihar.
Inda ya bayyana cewa rabon motocin aikin ga Alkalan wata shaida ce ta goyon bayan da gwamnatin jihar ke bayar wa ga bangaren shari’a wajen tabbatar da adalci ga al’umma.