Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad |
Gwamnan jihar Bauchi ya yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya saurari halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, da ya ce manufofinsa ba sa aiki kuma mutane suna shan wahala.
Da yake jawabi a lokacin da ya karbi bakuncin malaman addinin musulunci karkashin jagorancin Sheikh Sani Yahaya Jingir, gwamnan ya shawarci shugaban kasa da ya saurari ‘yan kasar ya kuma gyara kura kurai da ya yi.
Ya ce ya zama wajibi shugabanni su gaya wa kansu gaskiya yana fadar hakanne domin shugaban kasa ya gyara kuskurensa domin ’yan kasar suna shan wahala da su kansu gwamnoni suna shan wahala saboda tsauraran manufofin shugaban.