Gwamnan Bauchi ya bai wa ma'aikacin DW Hausa mukamin kwamishina

 

Usman Shehu Usman

A wani ci gaban fasaha, majalisar dokokin jihar Bauchi ta kafa tarihi, inda ta tantance mutum na farko da gwamnan jihar ya tura da sunan sa a matsayin kwamishina, Usman Usman Shehu, ta bidiyo ta manhajar Zoom.

Wannan ya nuna kudurin majalisar dokokin jihar na rungumar sabon tsari a cikin al'amuranta, da tabbatar da rungumar fasahar zamani cikin ayyukanta.

Usman Usman Shehu, wanda dan karamar hukumar Giade ne ta jihar Bauchi, ya fara karatunsa na farko da karatun Islamiyya kafin ya wuce makarantar firamare da sakandare a jihar. Ya ci gaba da neman ilimi har zuwa jami'a a yanzu yana zaune a kasar Jamus. Kwararran dan jaridar ya yi shekaru wajen 18 yana aiki da rediyon Jamus a matsayin babban edita.

Duk da an yi tantancewar ta hanyar Zoom a majalisar, amma ba a samu wata matsala ba, inda mambobin majalisar suka yi tambayoyi masu muhimmanci tare da samun ingantacciyar amsa daga Usman Usman Shehu.

Kawo yanzu ba a bayyana ma'aikatar da gwamnan na Bauchi zai tura sabon kwamishinan ba. 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp