Fadar shugaban shugaban Nijeriya ta ce gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali wajen inganta rayuwar 'yan kasa da kuma kyautata alakar kasar da da wasu kasashen.
Da yake martani kan kalaman Gwamnan Bauchi Bala Muhammad, mashawarcin Shugaba Tinubu kan yada labarai Sunday Dare, ya ce 'yan Nijeriya ne su ka zabe shugaban kuma ba zai mayar da hankalin kan masu suka ba da har su dauke masa hankali kan inganta rayuwar 'yan Nijeriya.
Sunday Dare ya shawarci Gwamna Bala da ya fuskanci aikin da ke gabansa maimakon bata sunan Shugaba Tinubu.
Category
Labarai