Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya ce gwamnatin jihar za ta rage farashin fetur ga manoma da ke yankunan da matsalar masu tada kayar baya ta shafa.
Zulum ya bayyana hakan ne a jiya Jumu'a, lokacin da yake kaddamar da kayan noma ga manoma 5000 da matsalar tsaro ta raba da gidajensu.
A cewar gwamnan, litar mai da ake saidawa N1,000 zuwa N1,200 a Maiduguri, za a bayar da tallafi don rage farashin ga manoma su rika samu N600, da manufar saukaka musu tsadar kayayyaki da kuma barnar da su ka fuskanta saboda matsalar tsaro.
Category
Labarai