Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da nadin Abdurrahman Ahmed Bundi a matsayin babban mai taimaka masa na musamman a fannin jaridu da sadarwa ta zamani (STA).
Kakakin gwamnan, Malam Dauda Iliya ne ya sanar da nadin a Maiduguri babban birnin jihar.
Abdurrahman Bundi ya kammala karatunsa ne a Jami’ar Maiduguri a shekarar 2011 sannan ya samu digirinsa na biyu a fannin gudanar da watsa labarai daga Jami’ar Middlesex da ke London.