Kowa ya ce wutar kara ta kwana......
Yadda wuta ta ƙone unguwar Pacific Palisades ƙurmus, da ke cikin birnin Los Angeles jihar California a ƙasar Amurka, ciki har da gidajen jarumai 35.
Zuwa yanzu mutum 10 aka tabbatar da mutuwarsu, sanadiyar wutar dajin, ibtila'i mafi girma da ya taɓa far wa birnin, inji shugaban hukumar kashe gobara na Los Angeles Kristen Crowley.
📸AFP News Agency