Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya EFCC da hukumar jami'an tsaron farin kaya DSS za su kashe naira biliyan biyu wajen saka mai ga motocinsu a shekara ta 2025, kamar yadda jaridar Punch ta gani a cikin kudurin kasafin kudi.
Kasafin naira tiriliyan 47.90 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa majalisa a Disambar bara, an ware tiriliyan 4.91 ga bangaren tsaro domin ingata ayyukan jami'an tsaro wajen yaki da ta'addanci.
Bincike ya nuna cewa an ware wa hukumar EFCC naira miliyan N808.7 domin shan mai, sai wasu N462m na ciye-ciye da tande-tande. Haka kuma hukumar DSS an ware mata naira biliyan N1.37 domin sayen fetur.
Category
Labarai