![]() |
Farfesa Abdallah Uba Adamu |
Farfesa Abdallah Uba Adamu ya yi Allah wadai da hakan ne a ranar Lahadi a wajen wani taron karawa juna sani na kwanaki biyu da aka shirya wa masu amfani da shafukan sada zumunta daga jam’iyyun siyasa daban daban a jihar Kano.
Taron wanda wata kungiya ta shirya tare da hadin gwiwar majalisar malamai ta Nijeriya reshen Jihar Kano, ya yi tsokaci kan wasu kafafen yada labarai da suka rika yada labaran karya domin tattaunawa a siyasance tsakanin ‘yan siyasa.
Sai dai Farfesa Uba Adamu , daga tsangayar sadarwa a Jami'ar Bayero ta Kano wanda shi ne babban bako a wajen taron, ya yabawa wasu wa'yanda suka shirya taron domin ilmantar da masu amfani da shafukan sada zumunta na zamani.