'Yan Nijeriya na kusa ga fuskantar karin kudin amfani da layukan sadarwa, inda ake hasashen farashin data 1GB zai iya kai N560.
Ministan sadarwa Bosun Tijani, yayin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels a kwanan nan, ya ce kamfanonin sadarwa ba zasu yi karin kudi kashin 100 ba sai dai kashi 30 zuwa 60.
Idan aka amince da karin na kashi 60, jaridar Punch ta lissafa cewa kiran wata duk minti daya zai tashi daga N11 zuwa N17.6, inda tura sako zai tashi daga N4 zuwa N6.4, yayinda farashin data 1GB zai karu daga N350 zuwa N560.
Category
Labarai