Dillalan mai karkashin kungiyar 'yan kasuwa ta PETROAN sun bukaci gwamnatin tarayya da ta miƙa matatun mai na Nijeriya ga kamfanoni masu zaman kansu domin samar da gogayya ta yadda bangaren mai zai ci gaba.
Kungiyoyin na son gwamnatin ta fara da matattun mai na Warri da Kaduna masu tace ganga 125,000 a kowace rana.
Dillalan man sun kuma yi kira ga gwamnati da ta karfafa amfani da iskar gas ta CNG da kuma magance safarar fetur da ake yi.
Category
Labarai