![]() |
Abdullahi Umar Ganduje |
Shugaban jam’iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana bukatar sojoji su kakkabe dazuka domin kawo karshen ‘yan ta'adda a Nijeriya.
Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar jajantawa ga gawamnatin jihar Neja, kan faduwar tankar mai da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a jihar.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Edwin Olofu, ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, shugaban jam’iyyar APC ya jaddada bukatar daukar matakan da suka dace da kuma daukar matakai masu tsauri, musamman ga masu aikata laifuka da suka buya a cikin dazuzzuka, don kawo karshen su a fadin kasar.