Dan wasan gaba na tawagar kwallon kafa ta Real Sociedad dake buga gasar La liga ta kasar Spain , Sadiq Umar ya kammala komawa tawagar Valencia CF dake kasar ta Spain a matsayin aro na wata shida.
Mai shekaru 26, dan wasan dan asalin jihar Kaduna kuma dan wasan gaba na tawagar Najeriya wato Super Eagles, ya koma ne bayan cimma yarjeniya da Valencia, a yayin da aka bude kasuwar musayar 'yan wasa a watan Janairu.
Sadiq zai yi amfani da riga mai lamba 12 a tawagar ta Valencia, abinda hakan ke zama wani sabon shafi ga dan wasan da yayi fama da jinyar raunin da ya samu a kakar shekarar bara ta 2023/24, wanda ya hana shi buga gasar kofin Afirka na AFCON, da Najeriya ta zo a mataki na biyu.
Category
Labarai