Dan wasan kungiyar Liverpool Mohammed Salah ya ce yafi son lashe gasar Premier ta kasar Ingila fiye da cin kofin zakarun Nahiyar Turai

Mohammed Salah

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Mohamed Salah, ya bayyana matukar sha’awarsa na lashe kofin gasar firimiyar kasar Ingila, inda ya bayyana cewa ya zarce burinsa na lashe gasar zakarun Turai a bana.

Da yake zantawa da dan jarida mai bibiyar harkokin wasanni Fabrizio Romano a ranar Juma'a, Salah ya ce, yana matukar son lashe gasar fiye da gasar zakarun Turai a wannan shekarar 2025.

Dan wasan dan asalin kasar Masar ya kuma yi sharhi game da ra'ayin shi na zama gwarzon duniya inda ya ce,ba karamin abu bane zama gwarzon duniya amma lokaci zai tabbatar da hakan.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp