Dan gwagwarmaya Kemi Seba ya bayyana aniyar sa ta takarar shugaban kasa a Jamhuriyar Benin

 


Fitaccen dan gwagwarmayar nan mai fafitikar cigaban Afirka dan kasar Bénin Kemi Seba, ya bayyana aniyar sa a hukumance ta tsayawa takarar shugaban Kasar sa a zaben badi na 2026

Kemi Seba da ya yi shuhura wajen caccakar wadan su shuwagabannin Afirka da yake dangantawa da karnukan farautar turawan yamma ya bayyana wannan aniya tasa ne ta kafar shafukan sada zumunta na zamani ta cikin wani faifen bidiyo da ya wallafa.

Dan fafutikar ya kuma yi fice wajen sukar salon mulkin wadan su shuwagabannin kasashen Afirka tare da yaba wa da salon kamun ludayyin shuwagabannin kasashen uku na kungiyar AES.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp