Mataimaki na musamman ga shugaba Bola Tinubu kan yada labarai Daniel Bwala ya mayar wa tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i martani, bayan da ya caccaki jam'iyyar APC.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na X, Bwala ya ce El Rufa'i ba zai yi wadannan kalaman ba da ya na cikin gwamnatin Tinubu.
Yayin wani taro a birnin tarayya Abuja, Nasir El Rufa'i ya ce yanzu baya ganin jam'iyyar ta APC a matsayin jam'iyya kasancewar ba ta bin tafarkin Dumokaradiyya.
Category
Labarai