Graham Potter |
Kungiyar kwallon kafa ta Wes Ham United ta tabbatar da nada Graham Potter a matsayin sabon mai horar da tawagar.
Ta cikin wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafinta na Facebook , kungiyar ta amince tare da cimma yarjejeniya da Potter na tsawon kwantiragin shekaru Biyu wanda zai kammala a 2027.
Nadin nasa ya biyo bayan sallamar da kungiyar ta yiwa tsohon mai horar da tawagar Julen Lopetegui dan asalin kasar Spain.