Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo ya bayyana cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi a matsayin wani abin alheri da ya samu gwamnatocin jihohin Nijeriya.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake duba wasu ayyuka da gwamnatinsa ke aiwatar wa a jihar.
Uzodimma ya ce yanzu haka jihohi na samun kudaden shiga da suke ayyukan ci gaban al'umma da su.