Bashin da ake bin Nijeriya ya karu zuwa naira tiriliyan 142 a watan Satumban 2024, abinda ke nufin an samun da naira tiriliyan 8 idan aka kwatanta da watan Yunin 2024 da bashin yake naira tiriliyan 134.
Wannan na kunshe ne a cikin kididdiga da ofishin kula da basussuka na Nijeriya ya fitar.
Jaridar Dailytrust ta ruwaito cewar, wannan ƙarin na nuna tasirin bashin cikin gida dake karuwa da kuma yadda faduwar darajar naira ke shafuwar bashin waje.
Category
Labarai