Bankin Duniya ya dakatar da wasu kamfanoni 2 na Nijeriya na tsawon watanni 30 bisa zargin zamba,cin hanci da rashawa

 

Bankin Duniya

Kamfanoni biyu da ke Nijeriya,sun hada da Viva Atlantic Limited da Technology House Limited, bankin ya dakatar da su ne na tsawon watanni 30 bisa zarginsu da zamba, cin hanci da rashawa.

A cewar wata sanarwa da bankin da ke Washington ya fitar dakatarwar ta shafi babban daraktan kamfanonin kuma babban jami’in gudanarwa, Norman Bwuruk Didam.

Binciken ya nuna yadda kamfanonin suka keta tsare tsaren Bankin Duniya ta hanyoyin wasu kwangiloli da suka yi a kamfanonin wanda hakan ya sabawa dokokin kamfanin da yasa aka dauki wannan mataki.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp