![]() |
Ministan Kwadago Muhammad Dingyadi |
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, a Nijeriya Muhammadu Dingyadi, ya ce bai da tabbacin kididdigar marasa ayyukan yi a kasar, amma ya sha alwashin ma’aikatarsa za tai kokari wajen magance rashin aikin yi.
Dingyadi ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da ayyukan yi da kwadago karkashin jagorancin Sanata Diket Plang.
Ya ce bai kai wata uku a ofishin sa ba, zuwa yanzu bashi da wata kididdiga ta marasa ayyukan yi,amma ma'aikatar na kokari wajen ganin an samu gurabe da samar da damarmaki a fadin kasar.